29 Afirilu 2021 - 13:59
Mutane 11 Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Bom A Kasar Somaliya

Kamfanin dillancin Labarun Faransa ya nakalto cewa; Bom din da aka sa a cikin wata mota wacce aka girke a kofar wani gidan kurkuku a yammaci birnin Magadishu, ya tarwatse, inda ya kashe a kalla mutane 11.

ABNA24 : Majiyar asibiti a yankin da lamarin ya faru ta ce, an kuma sami Karin wasu mutane da dama da suka jikkata.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin, sai dai akan danganta hare-hare irin wadannan ga kungiyar nan ta al-shabab mai alaka da Alka’ida.

Shekaru 7 kenan da kungiyar ta al-shabab take kai hare-hare a cikin kasar Somaliya da kuma wasu kasashen makwabta da su ka hada da Kenya.

342/